ilimi
Kano: Kotu ta bada umarnin buɗe Prime College

Wata Babbar Kotun Majistire da ke zamanta a unguwar Gyadi-gyadi a ƙwaryar birnin Kano, ta soke umarnin da ya rufe makarantar sakandare ta Prime College, inda ta bayar da umarnin a bude makarantar nan take.
Alƙalin kotun mai shari’a Fauziyya Sheshe, ce ta bada umarnin yayin zaman kotun na ranar Litinin din makon nan, inda ta ce, duk wani hani da Hukumar kula da makarantu masu zaman kansu da Malaman sa-kai ta jihar Kano PVIB, ta dogara da shi a umarninta na baya, an soke shi baki ɗaya.
Lamarin dai ya samo asali ne tun a ranar 16 ga Satumba, lokacin da hukumar ta PVIB ta shigar da ƙara kan makarantar bisa batun ƙarin kuɗin makaranta, wanda ya sa kotun ta bayar da umarnin wucin gadi har zuwa ranar 7 ga Oktoba, lokacin da za ta ci gaba da sauraron ƙarar.
A yayin zaman kotun, lauyoyin makarantar sun bayyana domin kalubalantar wannan umarni na dakatar da harkokin makarantar, inda suka ce an ɗauki matakin da bai dace ba.
Tun a watan Yuli ne dai Prime College ta sanar da yin ƙarin kuɗin makaranta, inda ta danganta shi da hauhawar farashin kayayyaki da kuma buƙatar ci gaba da samar da ingantacciyar koyarwa da gyaran makaranta.
Shugabancin makarantar ya ce, sama da kashi 94 cikin 100 na iyaye sun biya sabon kuɗin, duk da cewa wasu ƙalilan sun ƙi amincewa, tare da kai ƙara ga hukumar PVIB.
Hukumar ta PVIB ta kafa kwamitin wucin gadi da ya ƙunshi iyaye da malamai domin tattaunawa kan batun, inda yawancin su suka goyi bayan ƙarin kuɗin.
Amma daga bisani, hukumar ta ce, zaman bai kammalu ba, tare da bayar da umarnin a soke ƙarin kuɗin gaba ɗaya.
Daga nan ne kuma kotun ta bayar da umarni na dakatar da sabon tsarin kuɗin a ranar 17 ga Satumba, abin da daga baya wasu kafafen yaɗa labarai suka bayyana da cewa an rufe makarantar gaba ɗaya.
Sai dai Prime College ta ce wannan kuskuren fassarar umarnin kotu ne.
You must be logged in to post a comment Login