Connect with us

Labarai

 Kano: Majalisar zartarwa ta kafa kwamitin kwararru kan kafafan yada labarai

Published

on

A ya yin zaman majalisar zartar ta jiha ta amince da kafa kwamitin kwararru da zai duba rashin da’a da kuma kwarewa da wasu kafafan yada labarai na Kano ke yi.

A cewar sanarwar kwamishinan yada labaran na jihar Kano Kwamarre Muhammad Garba ne zai jagoranci kwamitin yayin da kuma a gefe guda za’a shirya taron masu ruwa da tsaki da ya hada da hukumar kula da kafafan yada labarai ta kasa NBC da hukumar tace fina-finai ta jiha da ma’aikatar shari’a da ta yada labarai da kuma shugabanin gidajen yada labarai na jiha.

Majalisar zartarwa ta amince da kashe biliyan 27 a ayyukan raya kasa

Kai tsaye: An dage cigaba da zaman majalisar Kano

Gwamnatin Kano ta ware fiye da Naira biliyan biyu domin gina asibitoci a sababbin masarautu

Ana dai zargin cewar wasu daga cikin kafafan yada labarai na jihar Kano da wuce gona da iri yayin da wasu ke ganin cewa wasu na da daurin-gindi shi yasa suke abun da suka ga dama.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,951 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!