Labarai
Kai tsaye: An dage cigaba da zaman majalisar Kano
Shugaban majalisar dokoki ta Kano Abdul’aziz Garba Gafasa ya dage cigaba da zaman majalisa zuwa gobe Talata don fara tantance kunshin sunayen da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya aike wa majalisar da safiyar yau Litinin.
Wakilin mu na majalisar dokokin Kano Abdullahi Isah ya ruwaito cewa, majalisar ta kuma bukaci wadanda aka aike da sunayensu domin nadasu a matsayin kwamishinonin da su zo habar majalisar a gobe Talata domin fara tantancesu
Sunayen da gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya aike sun hada:
Murtala Sule Garo
Engr. Muazu Magaji
Barrister Ibrahim Muktar
Musa Iliyasu Kwankwaso
Dr. Kabiru Ibrahim Getso
Mohammed Garba
Nura Mohammed Dakadai
Shehu Na’Allah kura
Dr. Mohammed Tahir
Dr. Zahara’u Umar
Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa
Sadiq Aminu Wali
Mohammed Bappa Takai
Kabiru Ado Lakwaya
Dr. Mariya Mahmoud Bunkure
Ibrahim Ahmed Karaye
Muktar Ishaq Yakasai
Mahmoud Muhammad
Muhammad Sunusi Saidu
Barrister Lawan Abdullahi Musa
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya aika da sunayen mutum 20 zuwa majalisar dokoki ta jiha domin tantance su da tabbatar da su a matsayin Kwamishinoni kuma yan majalisar zartarwa na Jihar Kano.
Kakakin Majalisa ne Abdu’aziz Garba Gafasa ya zaiyana sunayen a zaman majalisar da Safiya nan kuma ana sa ran fara tantancewar nan bada jimawa ba.
A dazun nan ne Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya aike da kunshin sunayen kwamishinonin da yake son nadawa don neman sahalewar su.
Daga cikin kunshin sunayen kawo yanzu da shugaban majalisar Abdula’aziz Garba Gafasa ya karantu cikin wasikar akwai tsohun kwamshinan Ayyuka na mussaman Musa Iliyasu Kwankwaso da tsohun kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo da Baba Impossible da Muntari Ishaq tsohun shugaban karamar hukumar Birni da Kewaye
Bayan da aka yi ta rade-raden da zarar ya dawo daga kasar Afrika ta Kudu zai nada kwamishinoni cikin kunshin Gwamnatin sa, kawo yanzu gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje bai sanar da ranar da zai yi wannan nadin ba.
A cikin karshen makonin da suka gabata ne aka yi ta ganin wasu kunshin sunayen tsofafi da sababin kwamishinoni, da wasu ke zargin sune kwamishinonin da Abdullahi Umar Ganduje zai nada.
Amma sai gashi sai yau Litinin ne 4 ga watan Nuwanba majalisar dokokin ta karbi wasikar kunshin sunayen kwamishinonin don neman sahalewar su.
Wakilin mu na majalisar dokoki ta jihar Kanop Abdullahi Isa ya rawaito cewa na cigaba da karantu sauran sunayen a yayin zaman majalisar na yau Litinin.