Labarai
Kano: Rundinar tsaro ta Neighborhood Watch ta sha alwashin tsare rayuka da dukiyoyi

Rundinar tsaro mallaki jihar Kano ta Kano Neighborhood Watch Security Agency, ta sake jaddada kudurinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.
Hakan na cikin wata sanarwar da daraktan yada labaran hukumar Yusuf Abubakar Ibrahim ya fitar ga manema labarai.
Sanarwar ta kuma ce Babban Kwamandan rundunar Laftanar Kanal Aminu Yusuf Abdulmalik mai ritaya, ya ce hukumar za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro da shugabannin al’umma don inganta tsaro, tare da kira ga jama’a su bayar da cikakken hadin kai, domin tsaro nauyi ne na kowa.
Ya kuma tabbatar wa ma’aikatan hukumar goyon baya domin karfafa ayyukan hukumar.
You must be logged in to post a comment Login