Kiwon Lafiya
Karamin ministan albarkatun mai ya ce Najeriya ta farfado daga asarar da ta yi na fiye da naira tiriliyan 1
Karamin Ministan albarkatun mai Dr, Emmanuel Kachikwu ya bayyana cewar gwamnatin tarayya na farfadowa daga asarar da ta yi na fiye da Naira tiriliyan 1 da ba’a biya daga cinkin danyen man fetur biyo bayan manofofin da ma’aikatar ta bullo na sanya biyan cinikin ta hanyoyin zamani.
Da yake amsa tambayoyi kan kudaden da aka tara na sabonta lasisi da ya kai fiye da Naira biliyan 1, Ibe Kachikwu ya ce ma’aikatar na kokarin gagauta samar da lasisi a Najeria ta hanyar saukaka hanyoyin da ake samar da shi.
Haka zalika a cewar ministan babban muhimman wajen samun wannan sauyin shi ne, sanya gaskiya a bangaren man fetur mussaman ma kan yanwa adadin gangar danyen mao da ake fitarwa a kullum.
Da yake yi wa manema labari Karin haske kan hukuncin da kamfanin mai zai dauka kan duk wani kamfani da ya gaza sabonta lasisin sa, karamin ministan mai ya ce kamfanin mai na kasa NNPC ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen soke lasisin duk wanda ya gaza yin hakan.