Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Karanbatta: Manchester United Ko Sevilla, wa zai samu nasara a wasan da za su yi?

Published

on

Daga Abdullahi Isa

Masu sharhi kan harkokin wasanni da dama suna da bambancin ra’ayi game da Kungiyar da za ta samu nasara a fafatawa da za ayi tsakanin Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da ke kasar Ingila da takwararta ta Sevilla da ke kasar Spaniya, a wasan daf da na karshe a gasar EUROPA ta nahiyar Turai.

Yayin da wasu ke ganin Manchester United za ta samu galaba akan Kungiyar Sevilla a bangare guda wasu gani suke ai Kungiyar Sevilla ba kanwar lasa bace musamman idan ana batu na gasar EUROPA.

Masu irin wannan tunani suna buga hujja da cewa Kungiyar Sevilla ta samu galaba akan Kungiyar Manchester United shekaru biyu da suka gabata adai wannan gasa ta Yuropa, inda bayan anyi canjaras babu ci tsakanin kungiyoyin biyu a zagayen farko a wasan da aka yi a ranar 21 ga watan Fabrairun shekarar dubu biyu da goma Sha takwas a kasar Spaniya sai Sevilla ta bai wa marada kunya inda ta doke Manchester United da ci biyu da daya har gida ta hannun dan wasa Ben Yadder.

Bugu da kari, masu irin wannan tunani suna buga kirji da cewa, Sevilla to goge sosai a wannan gasa ta Yuropa, inda a cikin wasanni da ta yi a baya bayan nan ta zarce kowace Kungiya lashe gasar cikin shekaru goma Sha biyar da suka gabata.

Sannan cikin wasanni na falan daya da ta yi 25 ta samu galaba a 24 daga cikinsu. Da wannan suke ganin Kungiyar Sevilla za ta iya samun nasara akan Manchester United.

Sai dai a bangare guda masu ganin baikin wannan ra’ayi suna cewa abin dariya ne ma mutum ya kwatanta abinda ya faru a wasa tsakanin kungiyoyin biyu a shekarar dubu biyu da goma Sha takwas a matsayin hujjar cewa hakan zai sake faruwa yanzu.

Hujjarsu kuwa ita ce ba waccan Manchester United da Sevilla ta samu galaba akanta bace, musamman ma suna ganin in ana maganar ‘yan wasa a halin yanzu kaf Duniyar nan babu wata kungiya da za ta yiwa Manchester United gori ko zarra musamman in ana maganar ‘yan wasa na tsakiya.

Haka zalika sun ce kamar yadda ake zaton Sevilla ta saba da wannan gasa ta Yuropa sosai a bangare guda Manchester United tana da dan wasa da ya san lagon gasar ta Yuropa wato Bruno Fernandez, wanda a yanzu haka duk da cewa dan wasa ne na tsakiya amma yafi kowanne dan wasa a gasar yawan kwallaye, inda ya zuwa kwallaye bakwai.

Har ila yau, masu ganin Manchester United ita ce za ta samu nasarar suna ganin cewa hazakar kungiyoyi bama daya bane a wannan lokaci. Musamman ganin zai matukar wahala yan wasan Sevilla su iya dakatar da Bruno Fernandez, Pogba, Greenwood, Rashford da Martial.

To koma dai me zai kasance Allah ne masani Kuma lokaci ne kawai zai tabbatar da gaskiyar lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!