Kasuwanci
KAROTA ta gargadi masu kasa kayan sayarwa a gadar Sabon Titi

Hukumar kura da Zirga-zargar ababen hawa ta Kano KAROTA, ta gargadi masu kasa kayayyakin sayarwa a gadar sama da ke Sabon Titin Ɗorayi.
Mataimakin Shugaban hukumar Auwal Lawan Shuʼaibu Aranposu, ne ya yi wannan gargadin yayin rangadin da ya kai gadar.
Tawagar tasa ta kewaya yankunan Hadejia Road da Kwanar Barde sai Hotoro da Zaria Road da kuma Gwarzo Road inda ya duba yadda ayyukan jamiʼan hukumar ke gudana.
You must be logged in to post a comment Login