Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Zamu fara kama baburan Adaidaita sahu -KAROTA

Published

on

Hukumar kula da zirga zirgar ababen hawa ta jihar Kano Karota ta ce daga sha biyun daren yau Laraba duk wani direban babur din adaidaita sahu da ya hau kan titin jihar Kano ba tare sabuwar lambar da hukumar Karota ta fara gudanarwa ba zai fuskanci fushin hukumar.

Shugaban Hukumar Karota Baffa Babba Danagundi ne ya tabbatar da hakan da yammacin yau Laraba a wani taron Manema Labarai da Hukumar ta kira domin kaddamar da fara sanya na’urar da zata rinka bibiyar duk inda abun hawa yake wato Tracker a jikin baburan adaidaita Sahu a fadin Jihar Kano.

Ya ce hukumar Karota ta kammala na sanya na’urar ta Tracker a jikin baburan Adaidaita Sahu kuma zata fara mallakawa duk wadanda suka yi sabuwar Lambar a gobe Alhamis tare da ba su katin shaida wato ID card.

Zamu fara kama motocin gidan gwamnati muddin suka gaza biyan kudin haraji -KAROTA

An dambata tsakanin KAROTA da Sojoji

 

Wakilinmu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito Shugaban hukumar ta Karota Baffa Babba Danagundi na cewa na’urar ta Tracker zata taimaka wajen zakulo masu aikata muggan laifuka da baburan adaidaita sahu domin gano mafakarsu don a hukunta su a kan laifin da suka aikata.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!