Labarai
An dambata tsakanin KAROTA da Sojoji
Da tsakar ranar yau ne wata hatsaniya ta barke tsakanin wasu jami’an sojoji da na ‘yan KAROTA a kan kwanar kasuwar Sharada inda kuma aka baiwa hammata iska.
Rahotanni dai sun bayyana cewa rikicin dai ya samo asali ne sakamakon aron hannu da ake zargin Sojojin sun yi don raste hanya, duk kuwa da cewa ba hannunsu bane, wanda kuma hakan ya sabawa doka, dalilin kenan da ya sanya ‘yan KAROTAR suka tare su.
Wasu shaidun gani da ido sun bayyana mana cewa ana tsaka da musayar yawu ne wani daga cikin sojojin ya doki dan karotar a ka har ya fasa masa kai.
Ko da muka tuntubi hukumar KAROTA don jin ko me hukumar za ta ce, jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yanzu haka ma maganar tana hannun ‘yan sanda.
An gurfanar da shugaban KAROTA a gaban Kotu
Hukumar KAROTA zata ware jami’an da zasu kula da cinkoson Safiya da dare
Jami’an KAROTA sun jikkata wasu matasa
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP Adullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da afkuwar al’amarin ga tashar Freedom Redio ya ce jami’in sojan yana hannun su yayin da kuma suke neman Mai Adai-Adaita sahun bayan ya da ya cika wandan sa da Iska
Wakilinmu Umar Lawan Tofa ya rawaito cewa rikicin ya fara ne daga Kwanar Kasuwar Sharada har ta kai zuwa kan titin Yahaya Gusau.