Labarai
Karya doka: Kotu ta ci tarar hukumomin tashar Kano Line
Kotun tafi da gidanka kan harkokin tsaftar muhalli ta jihar Kano, ta yanke hukuncin tarar Naira dubu ɗari biyu ga hukumomin tashar Motar Kano Line.
Kotun ƙarƙashin mai Shari’a Auwal Yusuf Suleiman ta yanke tarar ne da safiyar ranar Asabar, sakamakon samun tashar da laifin yin lodin fasinjoji lokacin da ake tsaka da duban tsaftar muhalli.
Laifin na su ya ci karo da dokar tsaftar muhalli, kamar yadda mai shari’ar ya bayyana.
Mai Shari’a Auwal Yusuf Suleiman ya ce, bayan samun tashar da laifin karya doka, kotun ta yi musu tarar Naira dubu dari biyu, haka kuma kotun ta ci tarar wasu direbobi biyu Naira dubu goma kowannen su, bayan ta same su suna lodi a haramtacciyar tashar mota da ke ƙarƙashin gadar Ado Bayero wadsa aka fi sa ni da Gadar Lado.
Jimillar tarar da aka ci na masu karya doka a yau ta kai dubu 309,600, kuma kimanin mutane 64 suka karya doka.
You must be logged in to post a comment Login