Connect with us

Labarai

Karya lagon boko haram ne ya sanya aka samu nasarar kubutar da yan matan chibouk-shugaba buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce karya lagon kungiyar Boko Haram ne ya sanya aka samu nasarar kubutar da yan matan chibouk 106 da kuma na sakandare Dapchi 104 wadanda mayakan na boko haram suka sa ce a baya.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne da safiyar Talatar nan lokacin da yake jawabi ga al’ummar Najeriya a wani bangare na bikin ranar dimokuradiyya ta bana da ke gudana a yau.

Ya kuma ce gano lago da maboyar yan Boko haram din shima ya taimaka wajen kubutar da sama da dubu goma sha shida da ke tsare a hannun mayakan na Boko Haram.

Ya ce kafin ya kama aiki a matsayin shugaban kasa ya iske kungiyar ta Boko haram ta kame garuruwa da dama da tambayar dasu karkashin ikon ta a yankin arewa maso gabashin kasar nan.

Muhammadu Buhari ya kuma yi alkawarin cewar gwamnatin sa ba zata huta ba har sai ta tabbatar da kakkabe dukkanin ayyukan yan ta’adda a kasar nan baki daya.

Ya kuma yiwa al’ummar kasar nan fatan alheri a lokacin da suke gudanar da bukukuwan ranar dimokuradiyya na bana.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,889 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!