Connect with us

Labarai

Kaduna:Akalla mutane 8 aka hallaka da jikkata 4 a rikicin da ya barke a kauyen Kurega

Published

on

Akalla mutane 8 aka hallaka yayin da aka jikkata 4 a wani rikici da ya barke a kauyen Kurega da ke karamar hukumar Chikum dab da iyakar karamar hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Lamarin dai ya faru ne da karfe biyu na ranar jiya Talata, wanda ake zargin barayin Shanu ne suka afkawa mutanen, inda kuma aka garzaya da wadanda su ka jikkata zuwa wani Asibiti mafi kusa da yankin

Wani jami’in rundunar Sintiri ta Vigilante ya tabbatar da mutuwar mutum 8, sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan-sanda ta Jihar Kaduna Aliyu Mukhtar Hussaini ya ce mutum 3 ne kacal su ka mutu yayin da aka jikkata mutum 4 yayin harin.

Haka zalika Aliyu Mukhtar ya bayyana cewa maharani sun yi awon gaba da Shanu da yawa, kuma tuni Rundunar ta fara gudanar da bincike a kan harin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,890 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!