Labarai
Kashim Shettima ya isa birnin Addisa-baba don halartar taron kungiyar AU

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, ya isa birnin Addisa-baba na ƙasar Ethiopia domin wakiltar Shugaba kasa Bola Tinubu a taron shugabannin ƙasashe kungiyar tarraya Afirka AU karo na 39 wanda za a gudanar daga gobe 14 zuwa 15 ga Fabrairu, 2026.
Taken taron shi ne tabbatar da wadatar ruwa mai ɗorewa da ingantaccen tsarin tsaftar muhalli, a wani yunƙuri na cimma manufofin ci gaban Afirka.
An tarbi Shettima a filin jirgin sama na Bole International Airport daga Ministan Ƙirƙire-ƙirƙire da Fasaha na Habasha, Belete Mola, da Mataimakin Ministan Harkokin Waje, Berhanu Tsegaye.
Haka kuma Ministan Harkokin Wajen kasar nan Yusuf Tuggar, da jami’an ofishin jakadancin Najeriya a Addis Ababa sun halarci tarbar, inda Tuggar ya yi wa Mataimakin Shugaban bayanin shirye-shiryen taron da ayyukan da zai gudanar.
A wata sanarwa da kakakin Ministry of Foreign Affairs Nigeria, Kimiebi Ebienfa, ya fitar, Tuggar ya ce kasar nan ta samu gagarumar nasarar diflomasiyya a taron majalisar zartarwa ta AU karo na 48, wanda ya ƙarfafa matsayinta a jagorancin haɗin kan tattalin arzikin Afirka.
You must be logged in to post a comment Login