Labarai
Kashim Shettima ya isa birnin Conakry na ƙasar Guinea, domin rantsar da sabon Shugaban ƙasar

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa birnin Conakry na ƙasar Guinea, domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a rantsar da sabon Shugaban ƙasar, Mamady Doumbouya.
A cewar mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Stanley Nkwocha, ya ce an tarbi Shettima da manyan jami’an gwamnatin Guinea da kuma wakilan jakadancin Najeriya.
Za a gudanar da bikin rantsuwar ne yau Asabar a filin wasa na GLC da ke Nongo.
Rantsuwar na zuwa ne bayan nasarar Doumbouya a zaɓen da aka gudanar a watan Disamban 2025, wanda ke nuna ƙarshen mulkin soji na tsawon shekaru huɗu a ƙasar.
Gwamnatin Najeriya ta ce halartar Shettima na nuna rawar jagorancin kasar a ECOWAS da kuma jajircewarta wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya, zaman lafiya da haɗin gwiwar tattalin arziƙi a yankin Yammacin Afirka.
You must be logged in to post a comment Login