Labarai
Kashim Shettima ya isa birnin New york don halartar taron MDD karo na 80

Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima, ya isa birnin New york domin halartar taron Majalisar Dinkin duniya karo na 80.
Shettima wanda ke wakiltar Shugaban kasa Bola Tinubu, zai gabatar da bayani a madadin Najeriya yayin babban taron muhawarar da za a gudanar inda zai bayyana sabbin gudummawar da kasarsa za ta bayar tare da halartar manyan tarurruka.
Mataimakin shugaban kasar ya samu tarbar daga ministan harkokin waje na Najeiya Ambasada Yusuf Tuggar da ministan tsaro Muhammad Badaru Abubakar da kuma wakilin Najeriya a ofishin Majalisar Dinkin duniya.
You must be logged in to post a comment Login