Labarai
Ketare: Falatsinawa na cigaba da gudun hijira zuwa Gaza
Dubban Falasdinawa a wannan Asabar sun ci gaba da yin gudun hijira daga arewacin Zirin Gaza zuwa kudancinsa, bayan da Isra’ila ta gargade su da su fice don tsira da rayukansu, kafin sojojinta su kaddamar da farmaki ta kasa kan mayakan kungiyar Hamas.
Yadda Falasdinawa ke tururuwar ficewa daga arewacin Zirin Gaza, bayan gargadin Isra’ila na shirin kaddamar da farmakin soji ta kasa kan kungiyar Hamas.
Fira Minista Benjamin Netanyahu ya yi gargadin cewa mako gudan da Isra’ila ta shafe tana kai hare-hare ta sama kan yankin na Gaza sharar fage ce kan martanin da za ta maida wa Hamas, wadda mayakanta suka kashe mata mutane sama da 1,300 a makon da ya wuce.
Ma’aikatar lafiyar yankin Falasdinu ta ce, zuwa yanzu mutane akalla dubu 1 da 900, akasarinsu fararen hula, da suka hada da yara sama da 600 Isra’ila ta kashe yayin ruwan bama-baman da ta ke yi a arewacin Zirin Gaza.
‘Yan Isra’ila, da wasu baki ‘yan kasashen ketare akalla 150 mayakan kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza, bayan kutsawa kasar ta Isra’ila da suka yi a ranar 7 ga watan Oktoba.
A ranar Juma’ar nan da ta gabata ne kuma kungiyar ta Hamas ta ce 13 daga cikin wadanda ta yi garkuwar da su sun mutu a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa ta sama.
You must be logged in to post a comment Login