Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Ɗalibai 5,000 ne suka rubuta jarabawar tantancewa a jami’ar YUMSUK

Published

on

Hukumar Jami’ar Yusif Maitama Sule ta jihar Kano bayyana cewa ‘Mata ne sukafi yawa cikin Dalibai dubu biyar da dari shida da suka zauna Jarrabawar tan-tance masu nemi gurbin karatu a Jami’ar da ta gudana yau Alhamis.

Mataimakin Shugaban Jami’ar Yusif Maitama Sule,Tijjani Rufai Buhari ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan duba yadda tantancewar ke gudana.

Malam Tijjani Rufai Buhari ya kuma Kara da cewar ‘har aka gama jarabawar ba’a samu rahoton wani dalibi ko daliba da aka samu da saba kaidojin da aka shimfida.

Wanda ya ce ‘hakan na nufin komai ya tafi yadda ake bukatarsa’.

A bangaren daliban da suka samu damar zana jarabawar sunyi fatan samun nasara yayin da jarabawar ta fito.

Freedom Radio ta ruwaito cewa hukumar Jami’ar ta ce ‘tana sa ran zata kammala duba Jarrabawar tantancewar tare da fitar da sakamakon cikin kwanaki biyar.

Rahoton: Abba Isa Muhammad

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!