Labarai
Tinubu ya shiga ganawar sirri da Ganduje da Kuma Hafsoshin sojin Nijeriya
A yammacin yau alhamis ne shugaba Bola Ahmad Tinubu yana ganawa da wata tawaga dake karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa Abdullahi Ganduje a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Duk da cewa har yanzu ba a bayyana makasudin taron ba, an rawaito cewa mahalarta taron za su gabatar da takarda mai dauke da muhimman shawarwari kan yadda za’a dakile rikicin manoma da makiyaya a fadin kasar.
Wata majiya ta ce an fara taron ne da misalin karfe 3:00 na yamma a agogon kasar ana gudanar da taron ne tare da hafsoshin tsaron Nigeria.
You must be logged in to post a comment Login