Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ko da gaske WhatsApp zai daina aiki?

Published

on

An wayi gari da wani labari cewa shafin WastApp zai daina amfani daga safiyar ranar Laraba.

Wannan labari dai ya tada hankalun al’umma da dama, da har ta kai ana yaɗa wata murya da ke gargaɗin cewa a tura wani sako kafin wannan rana ko kuma a rufe wanda bai ba.

To sai dai Freedom Radio ta gana da wani ƙwararre kan gano labaran bogi a shafin sada zumunta mai suna Aliyu Dahiru Aliyu da aka fi Sani da Aliyu Sufi, ya bayyana labarin amatsayin ƙanzon kurege.

Aliyu Dahiru ya ce labarin da ma an daɗe ana tura shi a shafukan sada zumunta tsahon shekaru da suka gabata wanda hakan ke sanya fargaba ga masu amfani da shafin.

“Idan za a iya tunawa a sanda Mark Zuckerberg ya sayi kamfanin WastApp a watan Fabrairun shekarar 2014, an ta tura makamancin sakon zuwa wayoyin mutane wanda mun san da cewa labarin ba gaskiya ne”.

“Yanayin yadda sautin muryar labarin da ake yaɗawa kamar ya nuna a kwanakinnan Zuckerberg ya sayi kamfanin, wanda mun san da cewa tsahon shekaru da suka gabata shi Zuckerberg ya sayi shafin na WastpApp”.

Aliyu Dahiru ya ci gaba da cewa “Abin da zai tabbatar da labarin na bogi ne shi ne yadda muryar da ake yaɗawa za ku fahimci haɗine na muryar na’urar kwamfuta, domin wanda yayi hakan ba yaso a fahimci muryar sace shi ne dalilin da ya sa ya aikata hakan domin ya sanya tsoro a zukatan al’umma”.

Wannan dai na zuwa ne bayan mako guda da shafukan Whattap da Facebook har ma Instagram suka katse, abinda ya bai wa wasu mutane damar tura saƙonni cikin harshen English da kuma sakwannin rubutu cikin yaren Hausa.

Abinda sakon ya ƙunsa:

“Gobe ƙarfe 6 za a rufe dandalin WhatsApp yanzu ki tura/ka tura wannan text ɗin wa mutum goma ko kuma su yi deleting ɗin contact ɗinki/ko kuma ko da an dawo yi to sai dai ki saya kuma za suna cire miki kudi”.

Sai dai masanin Aliyu Dahiru Aliyu ya shawarci al’umma da cewa saƙon da ake wallafawa su yi gaggawar watsi da shi domin kuwa ba shi da tushe ballantana makama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!