Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ko ka bayyana gaban mu ko mu gayyaci Buhari – Majalisar wakilai ga Mele Kyari

Published

on

Majalisar wakilan kasar nan ta ce matukar shugaban kamfanin man fetur na kasa NNPC Mele Kyari ya ci gaba da kin martaba gayyatar da ta masa, to ba ta zabi face gayyatar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

 

Shugaban kwamitin harkokin man fetur na majalisar Musa Sarkin-Adar ne ya yi wannan barazana a jiya alhamis lokacin sauraron ba’asin dalilin soke lasisin wasu kamfanonin hakar mai guda 4, wanda ya samu halartar karamin ministan mai Timipre Sylva.

 

Musa Sarkin-Adar ya ce tunda Mele Kyari ya gaza amsa gayyatar ta, to shugaba Buhari a matsayinsa ministan man fetur za su gayyata don amsa tambayoyi game da abinda ya shafi harkokin man a Najeriya.

 

Tun a ranar 23 ga watan Afrilun jiya ne dai shugaba Buhari ya umarci hukumar kula da albarkatun mai ta kasa DPR da ta janye soke lasisin kamfanonin da ta yi.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!