Labarai
Kogi: Yan Bindiga sun halaka jami’an tsaro da farar hula a harin shingen bincike

Yan bindiga sun kai hari a wani shingen bincike na ’yan sanda da ke jihar Kogi, inda suka kashe wasu jami’an tsaro tare da wani mutum da ke wajen.
Rahotanni sun ce maharan sun buɗe wuta ne kai tsaye kan jami’an da ke bakin aiki, lamarin da ya jawo tsananin firgici a wajen.
Hukumomin tsaro a jihar sun tabbatar da faruwar harin, tare da cewa an fara gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu a lamarin.
You must be logged in to post a comment Login