Labarai
Kotu ta ɗage shari’ar da ake yi wa tsohon Ministan Shari’a Malami

Babbar Kotun Tarayya da ke birnin tarraya Abuja ta ɗage shari’ar da ake yi wa tsohon Ministan Shari’a na Tarayya, Abubakar Malami da ɗansa Abdulaziz kan zargin ta’addanci zuwa ranar 10 ga Maris shekarar da muke ciki.
An ɗage shari’ar ne bayan Daraktan Gurfanar da Ƙara na Tarayya, Mista Rotimi Oyedepo, ya nemi karin lokaci domin su samu damar nazarin takardun shari’ar yadda ya kamata.
Oyedepo ya shaida wa kotun cewa kwanan nan aka miƙa shari’ar daga hannun Hukumar Tsaro ta DSS zuwa sashen Gurfanar da Ƙara na Tarayya, lamarin da ya sa ake buƙatar lokaci domin fahimtar cikakkun bayanai na shari’ar.
Lauyan wadanda ake tuhuma, Mista Adedayo Adedeji, bai yi adawa da bukatar dage shari’ar ba, Sai dai ya roki kotu ta soke karar idan masu gabatar da kara ba su fara shari’a a ranar da aka sake tsarawa ba, yana mai zargin rashin himma wajen bin karar yadda ya kamata.
You must be logged in to post a comment Login