Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta bada umarnin tsare tsohon shugaban KASKO a Kano

Published

on

Babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Hafsat Yahaya Sani, ta aike da Bala Inuwa Muhammed tsohon Manajan Daraktan Hukumar KASCO da dansa Bala Inuwa Muhammed (Jnr) zuwa gidan yari.

Laifukan da ake tuhumar su da su sun hadar da, karkatar da kudaden jihar Kano da suka kai Naira biliyan 3.2, da cin amana, da almundahana dama wasu da dama.

Daya daga cikin tuhume-tuhumen ya kasance tsakanin watan Agustan 2020 zuwa Afrilu 2023, Bala Inuwa Muhammed, tare da dansa da Incorporated Trustees of Associate of Compassionate Friend, sun karkatar da kudi N3,275,685,742.00 ba bisa ka’ida ba.

Tun da farko dai an raba kudin ne ga gwamnatin jihar Kano a matsayin tallafi daga asusun gwamnatin tarayya na KASCO, inda Bala Inuwa Muhammed ke rike da mukamin Manajan Darakta.

Har ila yau tuhume-tuhumen ya yi nuni da cewa, matakin da wadanda ake tuhumar suka dauka ya haifar da babbar illa ga jama’a da kuma gwamnatin jihar Kano, inda suka aikata laifin hada baki.

A lokacin da ake tuhumar su, Bala Inuwa Muhammed da dansa sun ki amsa laifin da ake tuhumarsu da su.

Lauyan wadanda ake kara, Farfesa Nasir Adamu Aliyu, SAN, ya bukaci kotun da ta bayar da belin wadanda ake kara domin samu kansu, inda ya bayyana yadda suke halartar zaman shari’a.

Sai dai mai gabatar da kara, wanda Barista Zaharaddeen Hamisu Kofar Mata ya wakilta, ya yi suka kan bukatar belin.

A hukuncin da ta yanke, mai shari’a Hafsat Yahaya, ta ki amincewa da bukatar mai kariya ta ki nbayar da belin nan take, inda ta bayyana cewa akwai bukatar a gabatar da bukatar belin na hukuma.

Don haka, ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake tuhumar har sai lauyan wadanda ake kara, Farfesa Nasir Adamu Aliyu SAN, ya gabatar da bukatar neman beli ga kotu.

Daga karshen dai an dage sauraron karar har zuwa ranar 6 ga watan Disambar 2023, don sauraren karar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!