Connect with us

Kiwon Lafiya

kotu ta bawa INEC damar cigaba da tattara sakamako a karamar hukumar Tafawa Balewa

Published

on

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta baiwa hukumar zaben ta kasa INEC damar ci gaba tattara sakamakon karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi.

Da yake yanke hukunci alkalin kotun mai shar’a Inyang Ekwo ya yi watsi da hukunci da ya bayar tun da farko na dakatar da tattara sakamakon.

Bayan jin bayanan da suka kamata ne kuma a yau litinin alkalin kotun ya baiwa hukumar INEC damar ci gaba ayyukan ta kamar yadda doka ta bata dama.

Jam’iyyar APC ce dai ta shigar da kara gaban kotun tana kalubalantar hukumar ta INEC da ta dakatar da karbar sakamakon karamar hukumar Tafawa Balewa bisa zargin tafka magudi.

Jam’iyyar dai ta shigar da karar ne tana kalubalantar hukumar ta INEC bisa ikirarin da ta yin a ci gaba da karbar sakamakon karamar hukumar bayan an ayyana zaben jihar a matsayin wanda bai kammala ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,603 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!