Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta umarci a zare ₦300,000 daga asusun kakakin ƴan sandan Kano

Published

on

bar Kotun tarayya da ke Kano ta bada umarnin a cire Naira dubu ɗari uku da aka samu a asusun banki na mai magana da yawun ƴan sandan Kano SP. Abdullahi Haruna Kiyawa.

Kotun ta ce, idan aka cire kuɗin za a a biya wani matashi Bashir Bashir Galadanci da su.

A shekarar da ta gabata ne Kotun ta umarci Abdullahi Kiyawa da ya biya Galadanci diyyar naira miliyan guda sannan ya shiga kafafen yaɗa labarai ya nemi afuwarsa, saboda ɓata masa suna da yayi.

Sai dai har yanzu Kiyawan bai cika waɗannan umarni ba, abin da ya sanya Galadanci ya sake komawa Kotun inda ta umarci a bincikin asusun bankin Kiyawan, inda aka samu dubu ɗari ukun.

Freedom Radio ta so jin ta bakin SP. Kiyawa amma har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto haƙanmu bai cimma ruwa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!