Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kotu ta yankewa matashi hukuncin kisa a Kano

Published

on

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 3 ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi mai suna Abba Mustapha.

Matashin mai shekaru 33 ana zarginsa da laifin kashe wani mai suna Buhari Abubakar sakamakon wani sabani da ya shiga tsakanin su, inda yayi amfani da Fatanya ya rika bugawa marigayin har ta kai hakan yayi sanadiyyar rasa ransa.

A yayin zaman kotun da ya gudana alkalin babbar kotun mai shari’a A.T Badamasi ya yankewa mai laifin hukuncin kisa, inda yace laifin da ya aikata ya sabawa sashi na 221, mai shari’ar ya kara da cewa lauyan gwamnati Barista Zakariyya Muhammad Garba ya gabatar da kwarararan hujjojin kan mai laifin.

RUBUTU MAI ALAKA:

Kotun daukaka kara ta soke zaben Alhassan Doguwa

Kotu ta yanke hukuncin kisan kai ga wani matashi a nan kano

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!