Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta yankewa wanda yayi fyade daurin shekaru 14 a Kano

Published

on

Wata babbar kotu da ke zaman ta a Bompai, ta yanke hukuncin daurin shekaru goma sha hudu ga Malam Nafi’u Abdullahi, mai shekarun Ashrin da Takwas, sakamakon yi wa wata yarinya fyade ‘yar shekarun hudu, a unguwar Kwarin Mallam da ke karamar hukumar Karaye.

Mai shari’a Namallam Sulaiman Baba ne ya yanke wannan hukuncin a zaman da kotun ta yi a yau Alhamis.

Haka zalika Mallam Nafi’u zai kuma biya tarar Naira dubu dari biyu baya wancan hukunci daurin, sannan ya kuma biya diya Naira dubu Hamsin ga yarinyar da ya yiwa fyade.

A cewar mai shari’a Namallam Baba, yanke wannan hukunci ga mallam Nafi’u Abdullahi an yi shi ne bisa dokar aikata laifin fyade.

Tun a ranar Ashirin ga watan Satumban shekara ta dubu biyu da goma sha hudu, aka kama Malam Nafi’u Abdullahi da aikata laifin fyade.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!