Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kotu ta yi watsi da karar bincikar masarautar Kano

Published

on

A yau Juma’a ne babbar kotun tarayya karkashin mai shari’a O.A Egwuatu ta yi watsi  da karar da  hukumar karbar korafe korafe ta jihar Kano daga cigaba da fitar da sakamakon bincike da hukumar take yi, dangane da zargin da hukumar keyi akan Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi na II da mutane 4.

Hukumar karbar korafe-korafen dai na zargin masarautar Kano ta kashe sama da Naira Biliyan uku da rabi ta hanyar da bai kamata ba, zargin da masarautar ta sha musantawa.

Matsalolin aure: Sarkin Kano ya bukaci a koma makaranta

Kano: zan tsoma baki kan rikicin Sarkin Kano da Ganduje – Buhari

Matsalolin aure: Sarkin Kano ya bukaci a koma makaranta

A dai kwanakin baya ne Sarkin Kano ya shigar da karar gwamnan Kano da babban mai shari’a na jiha kuma Antoni janaral kan zargin barnatar da wasu kudade da masarautar Kano ta yi.

Lauyan da yake kare sarkin wato Barrister Surajo Sa’ida SAN shine ya roki kotun da ta dakatar da Muhuyi Magaji da hukumar karbar korafi daga ci gaba da fitar da sakamakon binciken nan take kuma kotun ta amsa rokon.

Mai shari’a O.A Egwuatu ya kuma nemi hukumar ta karbar korafe-korafe karkashin jawagorancin Muhiyi Mgajin Rimingado da ta biya Naira dubu dari biyu a matsayin kudin diyya ga sarkin na Kano.

Wakilin mu na Kotu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewar, mai shari’a O.A Egwuatu ya sanya ranar 10 ga watan mayu na wannan shekarar don ci gaba da shariar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!