Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Kotun koli zata yanke hukuncin Abba da Ganduje ranar 20 ga watan Janairu

Published

on

Kotun koli ta saka ranar 20 ga watan Janairu domin yanke hukunci akan shariar kujerar Gwamnan Kano tsakanin Abba Kabir Yusuf da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

Jamiyyar PDP da dantakarar ta na gwamna a zaben shekarar 2019 Abba Kabir Yusuf ne suka shigar da karar a kotun koli.

Kotun koli tace zata yanke hukuncin ne bayan ta saurari bangarorin biyu da masu kare su .

Gwamnatin Buhari na bin umarnin Kotu- Abubakar Malami

Majalisar Sarakuna : Ganduje ya maida martani kan umarnin kotu

A dai ranar 2 ga watan Oktoba ne dai kotun sauraran kararrakin zabe ta Kano ta yanke hukunci akan zaben inda ta tabbatar da zaben gwamna Ganduje wanda hakan yayi dai dai da hukuncin kotun daukaka kara ta Kaduna.

Dalilin haka ne Abba Kabir Yusuf da jamiyyar PDP suka daukaka kara zuwa kotun koli.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!