Labarai
Kotun Koli zata bayyana ranar yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano
Kotun ƙoli ta ce za ta sanar da ranar da za ta yanke hukuncin ƙarshe kan shari’ar gwamnan Kano tsakanin gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP da Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC.
Kotun ta bayyana haka ne a yau Alhamis bayan zaman da ta yi na farko kan ƙarar da gwamna Abba Kabir ya shigar gabanta.
Gwamnan na jam’iyyar NNPP ya shigar da ƙarar domin ƙalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya tabbatar da hukuncin kotun sauraran ƙararrakin zaɓe da ta soke nasararsa tare da bayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.
A watan Nuwamba ne Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, babban birnin Najeriya ta bai wa tsohon mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna kuma dan takarar APC nasara a hukuncin da ta yanke game da zaɓen gwamnan jihar Kano.
Tun bayan hukuncin ake zaman ɗar-ɗar a jihar ta Kano, inda mutane suka rinƙa fitowa suna zanga-zangar nuna adawa da hukuncin.
A cikin watan Maris na 2023 ne Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri’u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri’u 890,705.
You must be logged in to post a comment Login