Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dalilan Kotu na bayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓe

Published

on

Kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan Kano, ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar ranar 18 ga Maris ɗin bana.

Kotun ta bayyana hukunci ne yau Laraba ta manhajar sadarwa ta Zoom.

BBC ta ruwaito cewa, Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, wadda ita ce shugabar kotun kuma jagoranci alƙalan kotun guda uku, ta ce, ta yanke hukunci ne bisa hujjar cewa an yi aringizon ƙuri’u 165,633, waɗanda aka gano ba su da sitamfi da kuma kwanan wata a ƙuri’un da Abba Kabir na NNPP ya samu.

Haka kuma ta ruwaito cewa, Tun farko a watan Maris ɗin 2023, hukumar zaɓen ta ce ɗan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya ci zaɓen ne da ratar ƙuri’a 128,900.

Abba Kabir Yusuf, in ji INEC ya samu ƙuri’u mafi rinjaye da suka kai 1,019,602, inda Nasiru Yusuf Gawuna da ke biye da shi, ya samu ƙuri’a 890,705.

Alƙalan kotun sun umarci hukumar zaɓe ta INEC ta janye shaidar cin zaɓen da ta bai wa Abba Kabir Yusuf, tare da gabatar da ita ga Nasiru Yusuf Gawuna.

Jam’iyyar APC ce dai ta shigar da ƙara a gaban kotun ta na mai ƙalubalantar nasarar da Injiniya Abba Kabir Yusuf, ɗin ya samu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!