Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kudin Makaranta na biya – Barawo

Published

on

Babbar kotun shari’ar Musulinci da ke kofar kudu karkashin jagorancin mai shari’a Ustaz Ibrahim Sarki Yola ta fara sauraron karar wani matashi da ake zargi da guduwa da wani babur shekaru biyu da suka wuce daga zuwa dani kafin a gama ciniki.

Tun da fari ana zargin Aliyu Adamu da laifin zanba cikin aminci ta hanyar neman Aminu ya shige masa gaba wajen sayan babur, bayan sun je wajen sayan babur din ne sai ya nemi a bashi dani, sai ya gudu da babur din tsawon shekaru biyu kenan, hakan yasa dole Aminu ya biya kudin babur din.

A zaman kotun na yau Litinin 15 ga watan Maris 2021 bayan mai Shari’a Sarki Yola ya karantowa Aliyu abun da ake tuhumarsa da aikatawa, nan take ya amsa laifinsa na guduwa da babur da aka yiwa kudi Naira dubu dari da sittin.

Haka kuma kuto ta waiwayi wanda ake kara Aliyu ko ina babur din da ya gudu da shi a yanzu, inda ya ce ya siyar da babur din ya biya kudin rijistar makarantarsa tun a wancan lokaci.

Aliyu ya kuma ce tun da lamarin ya faru ‘yan ajinsu sun hada masa kudin babur din naira dubu dari da sittin domin ya biya masu babur din kudinsu.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito cewa mai shari’a Ibarahim Sarki Yola ya bada umarnin zuwa da wanda ake kara Aliyu banki domin ya cire kudin da ya ce suna a asusunsa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!