Connect with us

Kiwon Lafiya

Kungiyar al’ummar Musulmin jihar Lagos ta bukaci Samar da kotun shari’ar mulsunci

Published

on

Kugiyar al’ummar Musulmi da ke jihar Lagos ta buka ci da a samar da kotun shari’ar musulunici da za ta dinga shari’a kan al’amuran da suka shafi addinin musulunci.

Kugiyar na mika wannan bukata ne a lokacin da suke tattaunwa da dantakar Gwamnan jihar a jam’iyyar AD mista Owolabi Salis a jiya laraba.

A cewar kugiyar al’ummar musulmi na bukatar a gina musu kotun addinin musulunci, duba da cewa a yanzu haka al’amaran musulmi na hannun wadanda ba musulmi ba ne a jihar, inda ya ce mafiya yan lokuta ba sa samun adalci.

Da ya ke maida jawabi Owolabi Salis Ya ce matukar aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar to kuwa zai kafa kwamitin da zai duba yadda  za a samar da kotun domin amfanin al’ummar musulmin jihar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,290 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!