Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar boko haram ta dawo da yan matan sakandaren Dapchi

Published

on

Rahotanni daga jihar Yobe sun ce kungiyar Boko-Haram ta dawo da ‘yan matan Sakandaren Dapchi wadanda ta sace su a ranar sha tara ga watan jiya na Fabrairu.

 

Wata mazauniyar garin Damaturu babban birnin jihar Yobe, ta shaidawa Freedom Rediyo ta wayar tarho cewa, ‘yan Boko-Haram din sun dawo da ‘yan matan ne cikin wasu kwamban motoci tara kamar yadda suka sace su tun da fari

 

Ta kuma ce al’ummar garin na Dapchi sun tsere zuwa cikin dazuka, bayan da suka ga kwambar motocin mayakan na Boko-haram sun shigo garin.

 

A cewar ta sai dai daga bisani da suka ga ‘yan boko-haram din sun fara sakin yarinya guda daga cikin ‘yan matan,  kafin nan suka karasa gaba cikin tsakiyar garin, inda suka saki sauran ‘yan matan, lamarin da ya sanya al’ummar garin suka fito daga maboyarsu suka barke da shewa.

 

Rahotanni sun ce sai da sojoji da ke garin na Dapchi suka janye daga yankin kafin mayakan na Boko Haram suka shigo garin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!