Connect with us

Kiwon Lafiya

Kungiyar dalibai ta Najeriya ta bukaci a rika gina makarantun masu bukata ta musamman

Published

on

Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta bukaci masu hannu da shuni da su rungumi dabi’ar gina makarantun masu bukata ta musamman a fadin kasarnan don saukaka musu wahalhalun da suke sha wajen neman ilimi.

Shugaban kungiyar na kasa kwamared Haruna Kadiri  ne ya bayyana hakan lokacin mika lambar girmamawa ga sakataren gwamnatin jahar Kano Alhaji Usman Alhaji.

Haruna Kadiri wanda ya samu wakilcin kwamared Usman Umar Usman ya ce sun bashi lambar karramawar ne bisa yadda makarantar sa ta masu bukata ta musamman ‘Usman International School’ take bayar da gudunmawa wajen koyar da masu bukata ta musamman.

A nasa jawabin sakataren gwmanatin Kanon Alhaji Usman Alhaji ya bayyana cewa ana gudanar da makarantar ne da nufin taimakawa ba don kudin da ake samu ba.

kungiyar daliban ta kuma karrama shugaban makarantar Malam Abdurrahman Bello Ibrahim saboda kwazon aikinsa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!