Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kungiyar DAPPMAN ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin makwanin biyu don biyan bashin da suke binta

Published

on

Kungiyar manyan Dillalan mai masu depo-depo ta kasa DAPPMAN ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin makwanni biyu da ta biya bashin da mambobinta ke bin gwamnatin wanda ya kai naira biliyan dari shida da hamsin.

Sakataren kungiyar na kasa Olufemi Adewole ne ya bayyana haka ga manema labarai ta cikin wata sanarwa jiya a Lagos.

Sanarwar ta ce kudaden raguwar basukan tallafin mai ne da mambobin-ta ke bin tsohuwar gwamnatin da ta gabata.

Mr. Olufemi Adewole ta cikin sanarwar dai ta ce bako shakka idan gwamnati ta gaza biyan basukan ‘yayan kungiyar zasu rufe dukkan-nin depo-depo dinsu domin tsunduma yajin aiki.

A cewar sa ‘yayan kungiyar a yanzu sun dogara ne da basuka da suke karba daga bankuna domin biyan albashin ma’aikatansu da kuma gudanar ayyukan yau da kullum.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!