Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Hukumar NAHCON zata mayar wa maniyatan da basu sami damar zuwa hajjin bara ba,naira miliyan dubu dari takwas da Ashirin

Published

on

Hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON ta ce, ta ware Naira miliyan dubu dari takwas da Ashirin, a matsayin kudaden da za a mayarwa maniyata da basu samu damar zuwa aikin hajjin shekara ta 2017 ba.

 

Wannan na kunshe cikin sanarwar da kakakin hukumar Malam Adamu Abdullahi ya fitar a jiya.

 

Sanarwar ta ce, daga cikin kudaden akwai Naira dubu dari da takwas da daya da Naira miliyan dubu dari biyu da tara, wanda ma’aikatar lura da aikin hajji ta kasar Saudiya ta dawowa hukumar NAHCON, don mayarwa maniyatan da basu samu damar zuwa hajjin ba.

 

A sanarwa ta ce, akwai sama da Naira miliyan daya da dubu biyar wanda za’a baiwa jihohin da basu samu ruwan Zam-Zam ba.

 

Hukumar ta bukaci wadanda abun ya shafa su je hukumar jin dadin alhazai jihohinsu don karba kudaden na su.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!