Kaduna
Kungiyar Dattawan Arewa sun yi Allah wadai da kalubalen tsaro da ya ke addabar yankin

Kungiyar Dattawan Arewacin kasar nan, sun yi Allah wadai da kalubalen tsaro da ya ke addabar yankin, inda suka yi kira da a dauki kwararan matakai don magance matsalar.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, kakakin kungiyar Abubakar Jiddere, ya yi Allah wadai da tabarbarewar tsaro da ake samu, dama kawo tasgaro ga tattalin arzikin a yankin.
Dattawan, sun kuma bukaci gwamnonin jihohi da su ba da hadin kai, tare da yin kira ga jami’an tsaro da su kawo karshen matsalar rashin tsaro da ya ke addabar arewacin kasar.
Abubakar Jiddere, ya bayyana matakan da aka dauka na farfado da tattalin arzikin Arewa, tare da neman hadin kan alummar yankin domin kawo karshen matsalar rashin tsaro a arewacin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login