Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba mu da masaniya a kan matakin da gwamnatin Kano ta dauka – Iyayen yara

Published

on

Yayinda gwamnatin Kano ta kaddamar da kwamitin bibiyar matsalar sace-sacen ‘yara a Kano, kungiyar iyayen yaran nan da aka sace ta ce har yanzu gwamnatin Kano bata tuntube su kan matakan da aka dauka.

Kungiyar ta ce kwamitin bincike da aka kafa tun farko be neme su ba ta yadda za su iya gabatar da bayanai kan yadda yaransu suka bata.

Sakataren kungiyar iyayen yaran Shu’aibu Attajiri ya shaidawa Freedom radio cewa ba su san yadda kwamitin ya gudanar da bincike, domin hasali ma su suka nemi kwamitin da kansu.

Ya ce har yanzu babu wata takardar gayyata da suka samu daga bangaren gwamnatin, ma’ana gwamnati da kwamiti su kadai suka yi kidansu suka yi rawarsu.

A cewarsa sun samu labarin kwamitin ya hada rahotonsa shi kadai ba tare da tuntubar kungiyar iyayen yaran ba, kuma haka nan suka mika shi ga gwamnati, don haka babu tsoma bakinsu a cikin aikin wannan kwamitin.

Shu’aibu Attajiri ya ce kwamitin shi kadai ya hada rahotonsa, kuma har yanzu ba su san me yake cikin rahoton ba.

Ya ce iya iyayen yaran da aka samu ne kadai kwamitin ya tuntuba, amma sauran iyayen yaran da har yanzu ba a kai ga gano inda ‘ya’yansu suke ba a bi ta kansu ba.

Aikin kwamitin shine zai gudanar da bincike yadda aka sace yara tun daga shekarar 2010 zuwa lokacin da aka gano yaran nan guda tara da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gano a garin Onitsha.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!