Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An mika yaran da aka sace ga iyayen su a Gombe

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra ta  ce ta mika yara biyu da aka sace su a jihar  da iyalan su, bayan da aka tabbatar da cewa  iyayen su ‘yan asalin jihar Gombe ne.

Rahotannin sun bayyana cewar, rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra ta sanar da cewa ta gano wasu yara biyu da ake zargin an sace su kuma an saida su a jihar ta Anambra.

Wannan dai shi ne karo na cikin wata guda da jami’an ‘yan sada suka gano makamanci irin wadannan nan aika-aika a jihar ta Anambra.

Tun da fari dai a farkon wannan watan na  Okotoba dake neman karewa rundunar ‘yan sandan Kano ta gano mutum tara  ‘yan asalin jihar nan da aka sace su kuma aka saida su a can jihar Anambra.

‘Yan sanda sun kara ceto yara biyu da aka sace a Anambra

Iyayen yaran da aka sace sun bukaci taimakon al’umma

An yiwa daya daga yaran Kano da aka sace fyade

Akan haka ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin da gudanar da bincike akan yadda aka sace yaran da kuma saida su a can jihar ta Anambra.

Kazalika gwamnatin Kano ta kafa kwamitin bincike kan yaran da aka sace su Arba’in da Bagwai bayan da aka saida su a jihar Anambra.

A dai ranar Juma’ar da t agabata ne kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra Haruna Mohammed ya sanr da cewar jami’an rundunar suka kama wasu mata uku da ake zargin sato wasu yara biyu sai dai ba’a san inda Iyayen  su, suke ba.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!