Kiwon Lafiya
kassosa ta jaddada kudurin ta na ci gaba da bunkasa kwalejojin kimiyya
Uwar kungiyar tsofaffin daliban kwalejojin kimiyya na Kano, KASSOSA ta jaddada kudurin ta, na ci gaba da bunkasa kwalejojin kimiyya dake nan Kano.
Shugaban kungiyar, Alhaji Mustapha Nuhu Wali ne ya bayyana haka a wajen taron bude baki da kungiyar ta shirya wa mambobin ta da saukar karatun kur’ani a kwalejin kimiyya ta Mairo Tijjani da ke nan Kano.
Alhaji Mustapha Nuhu Wali, ya ce, manufar su ita ce, hada kan ‘ya’yan kungiyar da kuma koyi da annabin tsira wajen ciyar da jama’a, a yayin watan Ramadan.
Alhaji Mustapha Nuhu Wali ya kuma ce, shakka babu uwar kungiyar KASSOSA za ta yi duk me yiwuwa wajen kawo sauyi a fannin kimiyya don haifar da al’umma da za ta rika fa’idantar da so.
Shi kuwa sakataren kungiyar Alhaji Hassan Abdulhamid Hassan ya bukaci sauran mambobin su na aji-aji su rungumi ta’adar taimakon juna a wani mataki na haifar da jama’a mai inganci.