Connect with us

Kiwon Lafiya

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi NULGE ta yi barazanar gudanar da zanga-zangar gama gari

Published

on

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa NULGE ta yi barazanar gudanar da wata zanga-zangar gama gari matukar majalisun dokokin jihohi dana tarayya suka yi watsi da dokar baiwa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin Kansu.

Shugaban kungiyar reshen jihar Kano Comrade Abdullahi Muhammad Gwarzo ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau.

Ya ce ko kadan ‘yayan kungiyar ba za su amince da ci gaba da kasancewar kananan hukumomi karkashin ikon jihohi ba.

Comrade Abdullahi Muhammad Gwarzo ya kuma nuna rashin jin dadin sa game da rahotannin da ke nuna cewa majalisar dokokin Kano taki amincewa da dokar.

Kungiyar ta kuma sha alwashin daukar wasu matakai masu tsauri matukar aka ki baiwa kananan hukumomin damar sarrafa kudaden su kamar yadda jihohi da gwamnatin tarayya ke yi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,462 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!