Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar matasan jam’iyyar APC ta buƙaci da a cire Ganduje daga shugaban jam’iyya

Published

on

Gamayyar kungiyoyin matasan jam’iyyar APC reshen jihar Kano sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa da su kori mukaddashin shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje saboda gazawarsa ta kawo Kano a zaben 2023 da ya gudana.

Matasan sun kuma yi kira ga jagoran tafiyar Kwankwasiyya na kasa a Najeriya Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso da ya dawo jam’iyyar APC domin amfanin ‘yan jam’iyyar da kuma al’ummar Najeriya.

Shugaban kungiyar Ho Sadiq Ali Sango ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ya gudana a ranar Lahadi 21 ga watan Janairun 2024.

A cewarsa, “Muna so mu yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da shugabannin jam’iyyarmu na APC da su kori shugaban jam’iyyar APC na riko na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, saboda gazawarsa wajen Nasarar Jam’iyar a jihar Kano a zaben gwamnan da ya gabata,” inji shi.

Ga cikakken bayanin shugaban “Muna so mu yi kira ga shugaban kasa kuma Bola Ahmed Tinubu, da ya gaggauta sauke Abdullahi Umar Ganduje daga mukamin shugaban jamiyyar APC na kasa, saboda gazawarsa wajen ganin APC ta yi nasara a jihar Kano, a zaben gwamna da ya wuce, har ma da rashin nasarar jamiyyar APC a kotunan karar zabe.

“Hakan ya nuna cewa Ganduje ya janyowa APC abun kunya a matakin jiha da kuma kasa baki daya, baya ga zarge-zarge masu karfi da ake dasu a kansa wanda suka shafi cin hanci da rashawa, wanda duk duniya ta shaida.

“Haka kuma Ganduje ya ci amanar ‘ya’yan jam’iyyar APC da magoya bayansa a jihar Kano, bisa yadda yayi ta yi musu romon baka da cewa zasu yi nasara a kotu, wanda daga karshe ta tabbata karya yake, bayan da kotun koli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin halastaccen gwamnan Kano.

Sannan kuma nadin da aka yi masa na Shugaban Jamiyyar APC na kasa ya saba wa tsarin shiyya-shiyya na Jamiyyar, wanda hakan ya nuna karara cewa ya kamata a baiwa shiyyar Arewa ta tsakiya mukamin Shugaban APC na kasa.

“Don haka muna neman Ganduje ya gaggauta sauka daga mukamin, sanan kuma kada Tinubu ya sake ya kara ba shi wani mukami, domin kuwa kara bawa Ganduje wani mukami zai zubar da kima da mutuncin gwamnatin Tinubu a idon duniya.

“Muna mika sakon jinjina Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) na kasa. Mun san irin gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar Kano da ma kasa baki daya.

“Mun kuma yarda da tasirin farin jininsa da tasirinsa a tsakanin talakawan jihar Kano.

Mun gaskata cewa shi mutum ne mai gaskiya, hangen nesa, da jajircewa.

“Don haka muna kira gare shi da ya dawo APC, don kasancewa jagoran APC a jihar Kano, domin kuwa a wannan yanayi da ake ciki shi kadai ne zai iya rike jamiyyar tare da dawo da martabarta a idon alumma.

“A shirye muke mu yi aiki da shi da kuma mara masa baya a kan manufofinsa na siyasa.

“A dai-dai wannan gaba, Muna son taya Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano murnar nasarar da ya samu a Kotun Koli.

“Mun amince da hukuncin kotun koli kuma mun dauke shi a matsayin kaddara. Muna rokonsa da ya yi aiki tukuru domin daukaka darajar rayuwar alummar Jihar Kano.

“Muna ba shi tabbacin hadin kai da goyon bayanmu a kokarinsa na ganin an samar da kyakkyawan shugabanci da romon dimokuradiyya ga alummar Jihar Kano.

“Daga karshe muna kira ga daukacin alummar Jihar Kano, ba tare da laakari da bambancin siyasa ba, da su rungumi zaman lafiya da juna, kasancewar dukanmu yanuwa ne, kuma jihar Kano ce a gabanmu. Muna kira ga alumma da su nisanci tashin hankali da kalaman batanci, sannan mu karfawa soyayya da taimakon juna, don samun ci gaba mai dorewa a jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!