Labarai
Kungiyar NAAT ta yi barazanar tafiya yajin aikin sai Baba ta gani
Kungiyar ma’aikatan dake aiki a dakunan gwaje-gwaje na Jami’o’in kasar Najeriya (NAAT), ta ce idan har gwamnatin kasar bata biya musu bukatun su ba nan da kwanaki uku za su tafi yajin aikin sai Baba ta Gani.
Shugaban kungiyar reshen Jami’ar Bayero dake jihar Kano Kwamred Hashim Abba Yakasai ne ya bayyana hakan, yayin zanga-zangar Lumana da suka gabatar a Jami’ar da safiyar yau Laraba 20 ga watan Maris din shekarar 2024.
Yadda Mambobin SSANU da NASU suka rufe ƙofar jami’ar Bayero
Hakan ya biyo bayan rike musu albashi na sama da watanni biyar da gwamnatin ta yi.
Sun Kuma ce za su rufe duk wasu da kunan gwaje-gwaje dana bincike dake fadin Jami’oin kasar, kuma bazasu budeba har sai gwamnati ta saurare su.
Kwamred Hashim Abba Yakasai ya Kuma ce sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku daga ranar Larabar kuma idan gwamnati bata dauki mataki a kai ba za su dauki mataki na gaba wato tafiya yajin aikin dindindin na sai Baba ta Gani
You must be logged in to post a comment Login