Connect with us

Labarai

Kungiyar PENGASSAN ta yi allawadai da kalaman dan takarar shugaban kasa

Published

on

Kungiyar manyan ma’aikatar man fetur da iskar gas ta kasa (PENGASSAN), ta yi allawadai da kalaman da wani dan takarar shugaban kasa ya yi na cewa, zai sayar da kamfanin mai na Najeriya NNPC matukar ya samu nasara a zaben kasa da za a yi a badi.

Shugaban kungiyar ta PENGASSAN Francis Olabode ne ya bayyana haka ga manema labarai, yana mai cewar; kungiyar za ta yi tirjiya ga duk wani yunkurin sayar da matatun man kasar.

Mr Francis Olabode ya kuma ce ko da wasa kungiyar ba za ta taba amincewa da duk wani yunkurin sayar da kadarorin da tattalin arzikin kasar nan ya dogara da shi ba.

Ya ce me zai hana maimakon a sayar da matatun man, kawai a mai da hankali wajen gyara su.

Abaya-bayan nan ne dai kafafen yada labarai suka ruwaito tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar na cewa; matukar ya samu nasara a zaben kasa da za a yi a  badi, zai sayar da kaso mafi yawa na kamfanin mai na kasa NNPC ga ‘yan kasuwa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!