Labarai
Kungiyoyin ma’aikata ta bukaci majalisun dokoki da su yi watsi da mafi karancin albashin naira dubu ashirin da bakwai
Kungiyoyin ma’aikata da dama sun bukaci majalisun dokokin tarayya da su yi watsi da kudirin dokar mafi karancin albashi na naira dubu ashirin da bakwai da fadar shugaban kasa ta turawa musu a jiya.
A wasu sanarwar da su ka fitar daban-daban, Kungiyar manyan ma’aikatan gwamnati ta (ASCSN), da kuma kungiyar malaman makaranta ta (NUT) sun bukaci majalisun biyu da su amince kawai da mafi karancin albashi na naira dubu talatin.
Kungiyoyin sun dage kan cewa babu gudu ba ja da baya game da zancen mafi karancin albashi na naira dubu talatin.
A jiya ne dai babban mataimakin na musamman ga shugaban kasa kan harkokin majalisar dattawa Sanata Eta Enang ya tabbatar da cewa, fadar shugaban kasa ta mika da kudirin dokar ga majalisun dokokin tarayya.