Connect with us

Labarai

‘Yar takarar shugaban kasa karkashen jam’iyyar ACPN ta janye daga takara

Published

on

‘Yar takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar ACPN Obiageli Ezekwesili ta janye daga tsayawa takarar shugaban kasa, a yayin zaben da za a yi a ranar goma sha shida ga watan gobe na Fabrairu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben ta Ozioma Ubabukoh ta fitar jiya a Abuja.

A cewar sanarwar Madam Obi Ezekwesili ta janye daga takarar ce domin taimakawa wajen yakar jam’iyyar APC da PDP a zaben da za a yia watan gobe.

Sanarwar ta kuma ruwaito tsohuwar ministar na cewa ta yanke shawarar ce sakamakon shawarar da al’ummar kasar nan mazauna gida dana wajen su ka bata.

Madan Obiageli Ezekwesili ta kara da cewa, cikin watanni uku da suka wuce ta yi ta gudanar da taruka da ‘yan takara daban-daban game da yadda za a dakile yunkurin jam’iyyar APC da PDP a zaben da za a yi a watan fabrairu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,465 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!