Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kurket :Namibia ta doke Najeriya a gasar Kurket ta Kwibuka

Published

on

Najeriya ta yi rashin Nasara a hannun kasar Namibia da yawan gudu 59, a wasan da aka fafata a babban Birnin Bostwana na Gabrone.

Namibia ta fara wasan da kafar dama, bayan da ta yi galaba a gudu 21 da rasa guda 03, kafin Najeriya ta doke ta da bugun tazara na sanda sau 01, ta hannun Abdulquadri Taiwo.

Sai dai a zagaye na biyu ‘yar wasa Joy Efosa tayi rawar gani bayan da ta samo Nasara da gudu 23 tare da rasa guda 04 .

Daga bangaren Namibia ‘yan wasa Yasmeen Khan da Kayleen Green sun samo nasarar makin gudu 29 , ya yin da Jurienne Diergaardt , ta samar da 15.

Najeriya ta maida martani ta hannun Abdulquadri Taiwo da Joy Efosa da suka samar da nasarar jefa bi biyu tare da gudu 19 cikin 24 , kafin zubar da guda hudu , inda Agatha Obulor da Racheal Samson suka samar da guda 01.

An kamma zagayen karshe Najeriya na da nasarar gudu 66 da faduwa 07 a cikin bugu 20 na mai maitawa, ya yinda Namibia ta samu galaba da gudu 125.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!