ilimi
Kwalejin Aminu Kano ta rantsar da dalibai 848 da ke yin karatun Digiri

Kwalejin shari’ar Musulunci ta Aminu Kano, watau Legal ta rantsar da dalibai 848 wadanda ke yin karatun Digiri na farko wanda makarantar ke gudanarwa a karkashin jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutsin-ma FUD.
Da ya ke ganawa da manema labarai yayin taron, shugaban kwalejin Farfesa Balarabe Abubakar Jakada ya bayyana cewa, wannan shi ne karo na biyu da kwalejin ta gudanar da taromn rantsar da daliban da suke yin karatun Digiri a karkashin jami’ar ta Dutsen-ma.
A nasa jawain, shugaban sashen karatun Digiri na kwalejin Dakta Yusuf Salisu Sani, ya bayyana cewa, za su kara bagatar da sabbin kwasakwasai a matakin na Digiri nan gaba kadan domin kara sama wa dalibai damar yin karatu cikin sauki inda yanzu haka kwalejin ke da dalibai da ke karatun Digiri a fannin darusassa guda 8.
Wasu daga cikin daliban da kwalejin ta rantsar din sun bayyana farin cikinsu kamar haka.
A nasa bangaren shugaban sashen koyar da harshen Hausa na kwalejin ta Legal Dakta Isma’il Aliyu Waziri, ya bukaci daliban da su kasance masu bin dokoki da ka’idoji musamman ma wadanda suka shafi jarrabawa.
You must be logged in to post a comment Login