Labarai
Kwalejin Barewa zata cika shekara 100 da kafuwa
Kungiyar tsoffin daliban kwalejin Barewa sun gudanar da taron tattaunawa kan yadda za su gudanar da bikin cikar kwalejin shekaru dari da kafuwa nan da makwanni biyu.
A yayin taron shugaban kungiyar Alhaji Nasir Ibrahim Dantiye ya ja hankalin daliban dake karatu a yanzu da su guji aikata laifin satar jarrabawa.
Dantiye ya ce satar jarrabawa na daya daga cikin abinda ke sawa mutum ya rasa albarka a karatun da yake.
Sai dai ya ja hankalin iyaye da su rika kula da tarbiyyar “ya”yansu musamman wajen sauke nauyin da Allah ya dora musu.
An kafa kwalejin ta Barewa a shekarar 1921 inda a shekara mai kamawa ta 2021 kwalejin za ta cika shekara 100 da kafuwa.
You must be logged in to post a comment Login